Sau nawa Real Madrid da Liverpool suka doke juna?

  • Abdulwasiu Hassan
  • BBC Hausa, Abuja
Liverpool za ta kara da Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Liverpool ta fi nasara a kan Real Madrid a tarihi, yayin da ita Real Madrid ta fi Liverpool cin kofin gasar zakarun Turai

A ranar Asabar din nan ne dai kungiyoyin kwallon kafa ta Real Madrid da Liverpool za su fafata wasan karshe na gasar zakarun Turai ta shekarar 2018.

Real Madrid ce ta fara kai wa wasan karshe na gasar bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Bayern.

Ita kuwa Liverpool ta samu zuwa wasa na karshen ne bayan ta doke Roma.

Sai dai kuma ba yau ba ne kungiyoyin biyu suka fara karawa a wasan kwallon kafa ba.

Tarihin karawar kungiyoyin biyu

Kuma kawo yanzu dai Liverpool ce ta fi yin nasara a kan Real Madrid a fafatawar da suka yi a baya.

Kungiyoyin dai sun fara haduwa ne a gasar European Cup ranar 27 ga watan Mayun shekarar 1981 inda Liverpool ta doke Real Madrid da ci daya da nema.

Daga nan kungiyoyin ba su sake haduwa ba sai ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2009 inda Liverpool ta sake doke Real Madrid da ci daya da nema a gasar zakarun Turai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lucas na Liverpool ya taba Marcelo na Real Madrid ranar 10 ga watan Maris ta shekarar 2009 inda Liverpool ta lallasa Real Madrid 4-0

A ranar 10 ga watan Maris na shekarar 2009 din ne dai Liverpool ta sake lallasa Real Madrid da ci hudu da nema a gasar ta zakarun Turai.

Sai dai kuma ita Real Madrid ta dauki fansa a fafatawar da suka yi ranar 22 ga watan Oktobar shekarar 2014 inda ta lallasa Liverpool ta ci uku da nema a gasar zakarun Turai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Marcelo na Real Madrid da Philippe Coutinho na Liverpool suna bin kwallo a kararwar da Real Madrid ta lallasa Liverpool da 3-0

Kazalika Real Madrid ta sake doke Liverpool a karawar da suka yi cikin gasar zakarun Turai ranar hudu ga watan Nuwambar shekarar 2014.

Wannan ya nuna cewa kawo yanzu Liverpool ta yi nasara kan Real Madrid sau uku yayin da ita Real Madrid ta doke Liverpool sau biyu a fafatawar da suka yi kafin ranar Asabar 26 ga watan Mayun shekarar 2018.

Daukar kofin gasar zakarun Turai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Real Madrid suna Murana bayan sun ci kofin zakarun Turai ta shekarar 2017 ta hanyar doke Juventus

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ita ce kungiyar da ta fi ko wace cin kofin na gasar zakarun Turai inda ta lashe kofin sau 12.

Bugu da kari, kungiyar ce ta lashe gasar sau biyu a jere, kuma za ta lashe gasar sau uku a jere idan ta yi nasarar a wasan ranar Asabar.

Kuma za ta yi kokarin cigaba da kasancewa mai rike da kofin a fafatawar da za ta yi da Liverpool a yau.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Liverpool sun ci gasar zakarun Turai a shekarar 2005 bayan sun doke AC Milan wadda ta fara cinsu kwallaye uku

Ita kuwa Liverpool ta ci kofin sau biyar a baya.

Tana fatan kasancewa daya daga cikin kungiyoyi kadan da suka taba cin kofin sau shida in ta yi nasara a ranar Asabar.

Shekarar 2005 ce shekarar da Liverpool ta ci gasar a karo na biyar.