Babu tabbas ko Salah zai tafi gasar cin kofin duniya

Salah da Ramos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yadda Ramos ya kai Salah kwance

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce raunin da Salah ya ji a gasar Zakarun Turai ya yi muni sosai, a yayin ake fargabar dan wasan ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

Ko da yake hukumar kwallon kafar Masar na da tabbacin cewa dan wasan zai murmure kafin soma gasar cin kofin duniya da za a fara a 14 ga Yuni.

Salah ya fice fili yana kuka bayan Sergio Ramos ya ma shi keta a wasan karshe da Real Madrid ta doke Liverpool 3-1.

"Raunin ya yi muni sosai," in ji Klopp.

"Yana kwance a asibiti za a yi hoton kafadarsa, raunin ya yi muni."

Amma a sakon da ya wallafa a twitter a ranar lahadi, Salah ya ce yana da tabbacin zai tafi Rasha.

A nata bangaren, hukumar kwallon Masar ta ce an yi wa Salah hoto, kuma ya nuna ya samu targade ne a kafadarsa, tare da bayyana cewa tana da tabbacin zai murmure kafin gasar cin kofin duniya.

Salah wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 44 a bana, ya yi kokarin ya ci gaba da wasa bayan ketar da Ramos ya yi masa ana minti 26 da wasa.

Amma dole daga bisani ya fice fili, inda Adam Lallana ya karbe shi.

Daga baya Ramos ya wallafa sakon fatan alheri ga Salah tare da masa fatan samun sauki, inda ya ce kwallo ta gadi haka.

Magoya bayan Salah ba su ji dadi ba

Salah wanda ya fi yawan cin kwallaye a Premier ya samu farin jini a kakar bana.

Magoya bayan dan wasan musamman a kasarsa Masar hankalinsu ya tashi, inda suke fatar dan wasan zai murmure da wuri domin jagorantar tawagar kasar a Rasha.

Masar za ta tafi gasar cin kofin duniya a karon farko bayan shekaru 28, kuma 'yan kasar na ganin Salah zai jagoranci kasar ga nasara.