Kalli Hotunan yadda Real Madrid ta yi bikin lashe kofi

Real Madrid

Real Madrid ta yi bikin murnar kofin gasar zakarun Turai da ta lashe karo na uku a jere a birnin Madrid.

'Yan wasan kungiyar sun zagaya birnin Madrid saman budaddiyar mota a ranar lahadi, dauke da kofin da suka lashe a ranar Asabar.

Real Madrid ta lashe kofin ne bayan ta doke Liverpool ci 3-1 a karawar karshe da suka fafata a birnin Keiv na Ukraine.

Karo na 13 ke nan da Real Madrid ta lashe kofin.

Sergio Ramos ne ya sauka da kofin na zakarun Turai bayan sun isa birnin Madrid daga Kiev.

Kaftin din Madrid Sergio Ramos da mataimakinsa Marcelo ne suka gabatar da kofin ga dimbin magoya bayan Real Madrid.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda tawagar Real Madrid ta gudanar da bikin:

Bayanan hoto,

'Yan wasan sun zagaya Madrid dauke da kofin da suka lashe

Bayanan hoto,

Zidane ya shiga sahun su Bob Paisley da Carlo Ancelotti da suka lashe kofin karo uku a matsayin koci

Bayanan hoto,

Real Madrid ita ce kungiya ta farko da ta lashe kofin sau uku a jere tun tun Bayern Munich a da lashe kofin sau uku a jere tsakanin 1974 zuwa 1976.

Bayanan hoto,

Shugaban Real Madrid President Florentino Pérez tare da Zidane da tawagar kungiyar

Bayanan hoto,

Karo na biyar ke nan da Ronaldo ke lashe kofin

Bayanan hoto,

Zidane ya yi amfani da zubin 'yan wasan da suka lashe kofin a kakar 2016/17 ba wani sauyi a karawar shi da Liverpool

Bayanan hoto,

Dimbin magoya bayan Real Madrid ne suka fito domin ganin 'yan wasan da kuma kofin da suka lashe