Najeriya ta buga kunnen doki da Kwango

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Atletico Madrid doke Najeriya da ci 3-2 a wani wasan sada zumunta a makon jiya

Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta tashi kunnen doki 1-1 a wani wasan sada zumunta da suka buga da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango ranar Litinin a birnin Fatakwal na jihar Rivers.

Ekong William ne ya fara zura wa Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango kwallo a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Kuma bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ne 'yan wasan Kwangon suka farke kwallon, inda wasa ya koma 1-1.

A makon jiya ne kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta Spaniya ta doke Najeriya da ci 3-2 a wani wasan sada zumunta.

Ana yin wasannnin sada zumuntar ne a wani bangare na shirye-shiryen da kasar ke yi domin tunkurar gasar cin kofin duniya, wadda za a fara a watan gobe a kasar Rasha.

Labarai masu alaka