An sace wa Nwanko Kanu naira miliyan hudu a Rasha

Kanu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kanu ya buga wani wasa na musamman da hukumar Fifa ta shirya na fitattun 'yan kwallo a ranar Lahadi

An sace wa tsohon dan wasan Najeriya Nwankwo Kanu dala 11,000 kimanin naira miliyan hudu a cikin jakarsa a karshen makon da ya gabata a kasar Rasha.

Jaridar The Moscow Times ta ruwaito cewa an yi wa dan wasan wannan gagarumar sata a cikin jakarsa, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa yankin Kaliningrad da ke kusa da gabar teku daga filin jirgin sama na Sheremetyevo.

Kanu mai shekeara 41 ya je Rasha ne don yin wani wasa na musamman da hukumar Fifa ta shirya na fitattun 'yan kwallo a ranar Lahadi, gabanin fara wasan Cin Kofin Duniya a ranar 14 ga watan Yuni.

Birnin Kaliningrad na daya daga cikin birane 11 na Rasha da zai dau bakuncin wasannin.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Rasha ta ce an kama wasu mutane biyu dauke da jakankuna, bayan da Kanu ya sanar da batan kudinsa da ya isa Kaliningrad.

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Intanet, ma'aikatar ta ce: "An gano wadansu mutum biyu wadanda suka sauke kayansa daga cikin jirgin da ya taso daga Landan zuwa Moscow, suka kuma sace kudi daga jakar fasinjan, kuma a yanzu haka an kama su an tsare."