Guardiola na da matsala da 'yan Afirka - Toure

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasa daya ne kawai aka fara da Yaya Toure (a hagu) a kakar 2017-2018

Kocin Manchester City Pep Guardiola "yana yawan samun matsala da 'yan Afirka", in ji tsohon dan wasan tsakiyar kulob din Yaya Toure.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast, wanda ya bar City a watan Mayu bayan ya shafe shekara takwas a kulob din, ya ce yana son ya karya yadda aka camfa Guardiola, mutumin da ya bayyana a matsayin mai "kishi".

Ya ce "Ina ganin mu 'yan Afirka ba a mu'amala da mu kamar yadda ake yi da wasu," in ji Toure a wata hira da ya yi da kafar France Football.

Zakarun gasar Firimiya, City, sun ki su yi tsokaci game da ra'ayin na Toure.

Kafin ya tafi, kulob din ya rada wa daya daga cikin filayen atisayensa sunan Toure, ya kuma bude wani katafaren taswirarsa a sansanin atisayen kungiyar.

A yanzu kulob din a shirye yake ya sayi dan wasan Aljeriya da aka haifa a Faransa Riyad Mahrez daga kungiyar Leicester City.

Toure, wanda dan wasan Ivory Coast ne, ya buga wasa a karkashin Guardiola a Barcelona na tsawon kaka biyu har zuwa lokacin da aka sayar da shi ga City a shekarar 2010 kan fam miliyan 24.

Ya lashe muhimman kofi shida a Ingila, amma wasa daya ne kawai aka fara da shi a gasar Firimiya a nasarar ta baya bayan nan da City ta samu- wasansu na gida na karshe da suka yi da Brighton.

Kafin wannan wasan, Guardiola ya ce: "Yaya ya zo nan a farkon tafiyar. Inda muke a yanzu (mun kai wurin ne) domin abin da ya yi."

Shi kuwa Toure ya ce : "Ban san me ya sa ba, amma ina tunanin yana kyashi na ne, ya dauke ni abokin hamayya. Kamar na tare mishi wani abu.

"Ya yi mini mugunta . Sai na ma fara tunanin ko ba don launin fata ta yake mini haka ba.

"Ba ni na fara magana game da wadannan bambance-bambancen ba. A Barca ma wasu sun yi wannan tambayar.

"A lokacin da muka gane cewa yana yawan samun matsala da 'yan Afrika a duk inda ya je, na yi wa kaina tambayoyi.

"Ina son in kasance wanda zai kawo karshen camfin nan kan Guardiola."

Labarai masu alaka