An tsawaita wa mata hutun haihuwa a Najeriya

Mai ciki Hakkin mallakar hoto Elvis

Najeriya ta tsawaita hutun haihuwa ga masu jego daga wata uku zuwa hudu.

Ministan kwadagon kasar, Chris Ngige, ne ya bayyana hakan a birin Geneva na Switzerland, inda ya kara da cewa gwamnatin kasar ta kara yawan hutun ne don mata su samu isasshen lokacin da za su shayar da jariransu sosai.

Haka kuma dokar, wadda aka yi wa kwaskwarima ta bukaci ma'aikatu da hukumomin gwamnati da ma'aikatu da kamfanoni masu zaman kansu da su samar da wuraren reno, ta yadda mata masu jegu za su samu saukin kula da jariran nasu bayan sun koma aiki.

BBC ta ziyarci sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja inda ta ji ra'ayoyin mata a kan hakan, kuma da yawan matan sun nuna jin dadinsu da farin cikin wannan "ci gaba" da suka ce an samu.

Sai dai wasu kalilan sun nuna cewa karin ba wani na a-zo-a-gani ba ne.

A yanzu dai matan za su dinga shafe wata shida kenan suna hutun haihuwa, idan suka hada da hutunsu na shekara.

Dokar dai ta kuma haramta hukumomin gwamnati ko ma'aikatu masu zaman kansu sallamar mata daga aiki saboda dalilan da suka shafi aure ko kuma haihuwa.

Sannan ta hana daukar duk wani mataki na ladabtarwa a kan mace a lokacin da take hutun haiahuwa har sai ta dawo.

Labarai masu alaka