Jami'an kwallon kafa fiye da 100 'sun karbi hanci'

Man taking money

Fiye da jami'ai 100 ne na kungiyoyin kwallon kafar Afirka aka nuna a wani hoton bidiyo suna take dokokin hukumar ta hanyar karbar cin hanci a wani bincike da aka fara.

Wakilin BBC ya ce cikin wadanda lamarin ya shafa har da babban alkalin wasa na kasar Kenya Aden Range Marwa, wanda ya sanar da hukumar FIFA cewa ba zai halarci Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Rasha ba.

Hakazalika akwai kuma shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Ghana Kwesi Nyantachi, wanda babban jami'i ne a tawagar kwallon kafa ta duniya Fifa.

Bidiyon ya nuna Mista Nyantachi yana sanya dala 65,000 cikin wata ledar yin sayayya, a matsayin kyauta daga wani mutum da ya nuna kansa a matsayin babban dan kasuwa da ke neman ya taimaka masa dan daukar nauyin kungiyar kwallon kafar Ghana a wasan Lig.

Dan jaridar kasar Ghanar nan Anas Aremeyaw Anas mai binciken kwakwaf shi ne ya bankado kuma ya kwashe shekara biyu yana gudanar da binciken.

Binciken Anas abu ne mai girma. Jami'ai fiye da dari da shugabaninsu sun karbi kudi daga dan jaridar da ke bincikin sirri.

Fiye da sau 150 ya biya kudade a wurare daban-daban yayin binciken.

Biyan kudaden ya faru ne kafin gasar Premier ta Ghana, da Gasar Zakarun Turai da kuma wadansu wasanni da suka shafi kasashen duniya.

Alkalan wasa sun karbi kudi daga hannun mutanen Anas, wadanda suka tunkare su a matsayin magoya baya, kafin fara wasanni da dama - da suka hada da sa'o'i kafin wasa tsakanin Ghana da Mali.

Anas bai taba nuna fuskarsa a bainar jama'a ba.

Sai dai wadansu na kalubalantar dubarun aikinsa na jarida, musamman yadda yake nadar bidiyo a asirce.

Sai dai ya musanta ra'ayin cewa, yana bin dubaru ne na janyo ra'ayin mutane, yana mai cewa duk wadanda suka karbi kudi ba tursasa masu aka yi ba.

Mista Nyantachi ya ki amincewa ya yi magana da BBC, yayin da Fifa ta ce Mista Marwa ya janye daga cikin tawagar da za su yi alkalanci a gasar cin kofin duniya ta bana.

Shi kuwa alkalin wasa na Gambiya Ebrima Jallow, ya musanta cewa ya karbi wani kudi ta hanyar da ba ta dace ba.

Wata sanarwa da Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana ta fitar, ta ce ta nemi kamfanin da ya wallafa bidiyon da ya ba ta domin ta yi nazari a kai, san nan ta ce za ta dauki mataki kan duk wanda ya aikata ba daidai ba.

Labarai masu alaka