Patrick Vieira ne sabon kocin kungiyar Nice

Patrick Vieira Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Patrick Vieira yana cikin 'yan wasan Arsenalk din da suka ci gasa biyu a kaka daya tare da kasancewa daya daga cikin 'yan wasan da suka yi wasa a gasar 2003-04 ba tare da shan kaye ba

Tsohon dan wasan wanda ya taba yin wasa a kungiyoyin Manchester City da Inter Milan da Juventus yana cikin kakarsa ta uku ne a matsayin kocin kungiyar New York City a kasar Amurka, kafin samun wannan sabon mukamin.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Patrick Vieira ya zama kocin New York City ne a watan Janairun shekarar 2016

Sai dai gabanin nadin nasa, wadansu suna ganin Vieira, mai shekara 41, yana daya daga cikin mutanen da za su iya maye gurbin Arsene Wenger a Arsenal.

"Yanke shawarar barin kungiyar New York City abu ne mai matukar wahala gare ni da kuma iyalina," in ji Vieira.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Patrick Vieira, kamar Arsene Wenger, ya koma Arsenal ne a shekarar 1996 daga AC Milan. Ya buga wa kungiyar wasannin gasar Firimiya 279

Kungiyar Nice kare kakar Gasar Ligue 1a matsayi na takwas ne, wato maki daya tsakaninta da samun tikitin zuwa Gasar Europa.

Vieira zai maye gurbin kocin kungiyar Lucien Favre wanda aka nada kocin Borussia Dortmund a watan Mayu.

Tsohon dan wasan kasar Faransa, Vieira yana daya daga cikin 'yan wasan kasar da suka lashe Kofin Duniya a shekarar 1998.

Labarai masu alaka