Za a iya hasashen kasar da za ta lashe gasar kofin duniya a Rasha?

France, Germany, Brazil, Portugal, Argentina, Belgium, Poland, Russia, Peru, Morocco, England, Colombia, Nigeria, Costa Rica, Serbia, Saudi Arabia, Spain, Australia, Senegal, South Korea, Iran, Denmark, Sweden, Japan, Croatia, Mexico, Switzerland, Tunisia, Panama, Uruguay, Egypt, Iceland

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Kasashe 32 za su fafata a gasar cin kofin duniya

Kasashe 32 ne za su fafata, amma a karshe kasa daya ce za ta yi nasara.

Amma ta yaya za ka yi hasashen tawagar da za ta dauki kofin duniya a birnin Moscow ranar 15 ga watan Yuli?

Ta hanyar nazari kan salo da alkaluma da kuma tarihi na gasar da aka gudanar a baya, sashen wasanni na BBC ya zubar da kasashe 31 inda ya zabi kasa daya da ya yi hasashen za ta lashe kofin gasar.

Ga abubuwan da suka wajaba kasasashe da suka lashe gasar cin kofin duniya su yi...

Matsayin kasashe

Tun da aka kara yawan kasashen da ke buga gasar kofin duniya zuwa 32 a shekarar 1998, kusan dukkan kasashen da suka ci gasar sun kasance kasashe ne da aka ware.

Bugu da kari kasa ta karshe wadda ta ci gasar ba tare da an ware ta ba ta yi hakan ne a shekarar 1986, a lokacin da Ajantina ta dauki kofin ta hanyar kwallon da Diego Maradona ya ci da hannu.

Ta wannan hanyar mun cire tawagogi 24 daga cikin gasar, lamarin da ya bar mu da tawagogi takwas.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Kasashen Turai za su fi taka rawar gani - Hasashe

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Rashin kasancewa mai masaukin baki

Rasha ta ci arzikin al'adar gasar ta tsawon shekara 44 inda ake ware kasa mai masaukin baki.

Kasancewa kasa ta 66 a cikin jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, ba za ta kasance daya daga cikin kasashe takwas da ke kan gaba idan ba a kasarta ake gasar ba.

Karbar bakuncin gasar kofin duniya ba ya cikin hanyoyin da ake ganin za su kai ga kasa ga nasara kamar yadda tarihi ya nuna.

Gasa sha daya na farko da aka gudanar, daga shekarar 1930 zuwa shekarar 1978, kasashen da suka karbi bakunci gasar biyar ne suka yi nasara.

Tun wancan lokacin, a gasar tara da aka yi a baya sau daya kasar da ke karbar bakunci ta yi nasara - wato gasar da Faransa ta karbi bakunci a shekarar 1998.

Ya kasance abu mai wuya ga Amurka da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Afrika ta Kudu su ci gasar, a gasar Italiya 1990 da Jamus 2006 da kuma kasar Brazil a shekara hudun da suka wuce dukkacinsu karbar bakuncin gasar bai ba su damar lashe gasar ba.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Za a fitar da Rasha a wasan dab da kusa da karshe

Iya tsare gida da kyau

A lokacin da ake buga gasar tsakanin kasashe 32, babu daya daga cikin zakaru biyar na wannan lokacin da aka ci fiye da kwallaye biyar cikin wasanninsu biyar.

Idan aka kwatanta kasashe bakwai da suka rage, Poland ce ta fi samun koma baya a tsaron gida.

Ma'aunin yawan kwallayen da aka ci Jamus da Portugal ya kai 0.4 a ko wane wasa, ma'aunin Belgium da Faransa kuma shi ne 0.6 a ko wane wasa, Brazil kuma 0.61 a ko wane wasa na Ajantina 0.88 a ko wane wasa.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Faransa da Belgium da Jamus da Portugal da Brazil da Argentina za su kai zagayen dab da na kusa da karshe. Hasashe

Kasancewa daga Nahiyar Turai

Masu cin gasar kofin duniya daga nahiyar Turai da kuma kasashen kudancin Amurka suke fitowa.

Sai a baya-bayan nan ne kasashen Turai suka zaburo, amma nasarar Spain a Afrika ta Kudu da kuma Jamus a Brazil ya sauya wannan salon.

Akasari wadanda suke karbar bakunci gasar da ake yi a Turai su suke samun nasara.

A gasa cin kofin duniya 10 da kasashen Turai suka karbi bakunci, gasa daya ce kawai wata kasa daga wajen nahiyar ta Turai ta ci, kuma sai an koma shekarar 1958 inda Brazil ta ci gasar a Sweden.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Faransa da Belgium da Jamus da Portugal za su buga wasan dab da karshe - Hasashe

Sai idan kana da kwararren gola

Za ka iya tunanin cewa masu cin kwallo ne ke cin gasar cin kofin duniya, amma sau biyu ne kawai aka samu wanda ya ci kyautar zura kwallo ta takalmin zinari a tawagar kasar da ta dauki kofin tun shekarar 1982- Ronaldon Brazil a shekarar 2002 da kuma David Villa na Spain a shekarar 2010.

Masu cin kofin duniya sun fi siffantuwa da mai tsaron gidansu, inda ake samu hudu daga cikin wadanda suka ci kyautar gwarzon mai tsaron gida biyar suka kasance 'yan tawagar da suka dauki kofin.

Daga cikin kasashe hudun nan da suka rage ba zaka yi mamakin idan daya daga cikin su Manuel Neuer (Jamus) da Hugo Lloris (Faransa) ko kuma Thibaut Courtois (Belgium) ya kasance an fitar da sunansa a matsayin gwarzon mai tsaron gida a wannan lokacin.

Abu ne mai wuya a ce mai tsaron gidan Portugal, Rui Patricio, zai ci kyautar gwarzon mai tsaron gida.

Faransa da Belgium da Jamus da Portugal za su buga wasan dab da karshe - Hasashe

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Faransa za ta doke Portugal a matsayin na uku - Hasashe

Kasance kwararre

Kasashen da suke cin gasar kofin duniya suna ci gaba da zama kwararru, wani salon da ya fara a lokacin da aka fadada yawan kasashen da ke shiga gasar zuwa 32 a shekarar 1998.

A wancan lokacin, kasar Faransa da ta dauki kofin ko wane dan wasanta ya taka mata leda kimanin sau 22.77.

A shekaru hudun da suka gabata, ko wane dan wasan Jamus ya yi mata wasa sau 42.21. A tsakiyarsu an samu kari a hankali -taka ledar ko wane dan wasan Brazil ya kai 28.04 a shekarar 2002.

'Yan italiya sun taka leda 32.91 gasar a shekarar 2006, Spain kuma sau 38.30 a shekarar 2010.

A lokacin da sauran tawagogin ukun suka fitar da sunayen 'yan wasansu, yawan wasannin da ko wane dan wasan Faransa ya haska ya kai 24.56, yayin da na Jamus ya kai 43.26, na Belgium ya kai 45.13.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Belgium da Jamus za su buga wasan karshe - Hasashe

Kasar da ba ta rike da kofi

Yana da wahala kasar da ta ke rike da kofin duniya ta iya kare kofin.

Wannan ya kasance haka ne tun lokacin da Brazil ta ci gasar sau biyu a jere tsakanin shekarar 1958 da shekarar 1962.

Kuma tun da Brazil ta dauki kofin sau biyu a wancan lokacin, sau biyu ne kawai aka samu mai rike da kofi da ta wuce matakin kusa da dab da na karshe cikin kasashe 13 da suka taba cin kofin.

Ajantina a shekarar 1990 da Brazil a shekarar 1998, duk da cewa Brazil ta zama ta hudu a shekarar 1974 a lokacin da matakin rukuni na gasar ya kasance guda biyu kafin wasan karshe.

A gasar cin kofin duniya hudu da suka gabata, sau uku aka fitar da kasar da ke rike da kofin a matakin rukuni.

Jamus tana da tarihi mai kyau game da kofin duniya a baya bayan nan. A cikin gasa tara da suka wuce - ciki har da ukun da suka yi a matsayin yammacin Jamus- sun ci gasar sau biyu, sun kai ga wasan karshe sau uku kuma sun kasance na uku a gasar sau biyu.

Sai dai kuma, idan ana maganar sake cin kofin ne a Rasha, tarihi ba ya tare da su.

Saboda haka, bayanin ke nan. Belgium za ta ci kofin duniya. Sai idan wani ya ci kofin wanda kuma abu ne mai yiyuwa.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Belgium za ta lashe kofin duniya a Rasha - Hasashen BBC

Tasiwrar hoto: Katie Moses da Andrew Park na sashen wasanni na BBC