Barar da fanareti ba dadi - Messi

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda Lionel Messi ya barar da fanareti a wasan Argentina da Iceland

Latsa hoton sama don kallon yadda Messi ya barar wa Argentina da fanareti

Lionel Messi ya ce ya ji zafin fanaritin da ya barar wa Argentina a wasansu da Iceland a gasar cin kofin duniya.

Golan Iceland ne Hannes Halldorsson ya kabe fanaretin da Messi ya buga wanda ya haramtawa Argentina samun narasa a kan Iceland.

Iceland ta rike Argentina ne 1-1 a wasan farko da suka buga a rukuninsu na D wanda ya kunshi Croatia da Najeriya.

Croatia ce ke jagorantar rukunin da maki uku bayan ta doke Najeriya 2-0.

Messi ya yi kokarin nuna bajintar Ronaldo wanda ya a wasan farko da ya jagoranci Portugal ya ci kwallo uku shi kadai.

"Da abubuwa sun sauya domin ma ce muka samu," in ji Messi.

Ya ce ba ya jin dadi idan ya barar da fanareti. "Mun ji zafin rashin samun maki uku domin farawa da nasara yana da matukar amfani, yanzu muna tunanin haduwarmu da Croatia."

Messi yanzu ya barar da fanareti hudu daga cikin guda bakwai na baya-bayan nan da ya buga wa kulub din sa da kuma kasarsa Argentina.

A ranar Alhamis Argentina za ta hadu da Croatia, yayin da Najeriya kuma za ta fafata da Iceland, karawar da za ta tantance makomar Najeriya a gasar a bana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Goland Iceland Halldorsson ya haramtawa Messi cin faneri