Jamus ta sha kashi a hannun Mexico 0-1

Jamus da Mexico Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lozano ne ya ci wa Mexico kwallo a ragar Jamus

Jamus ta fara gasar cin kofin duniya da kafar hagu bayan ta sha kashi a karawarta da Mexico.

Mexico ta samu sa'ar Jamus da ke rike da kofin duniya 0-1.

Ana minti 35 da wasa Lozano ya zura wa Mexico kwallo a ragar Jamus.

Yanzu Mexico da ke rukuni guda da Koriya ta kudu da Sweden da kuma Jamus ta dare teburin rukuninsu na F da maki uku.

A gobe ne Sweden za ta fafata da Koriya ta kudu.

Sakamakon wasan ya nuna akwai kalubale a gaban Jamus musamman idan daya daga cikin Sweden ko Koriya ta kudu ta samu nasara a kan daya.

Wasu na dai na ganin doke Jamus a wasan rukuni na farko kamar Mexico ta tsallake ne zuwa zagaye na gaba.

A ranar 23 ga wata ne Jamus za ta buga wasanta na biyu tsakaninta da Sweden, yayin da Mexico za ta kara da Koriya ta Kudu.