Sweden ta fara gasar kofin duniya ta hanyar doke Koriya ta Kudu

Andreas Granqvist Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andreas Granqvist shi ne dan Sweden na farko da zai fara cin bugun fenareti da aka bayar a gasar cin kofin duniya tun lokacin da Henrik Larsson ya ci Najeriya ta bugun fenareti a shekarar 2002

Sweden ta doke Koriya ta kudu a wasanta na farko da ta yi a gasar kofin duniya tun shekara 12 da suka wuce ta kafar keftin dinta, Andreas Granqvist, wanda aka bai wa fenareti ta hanyar bidiyo.

An samu wani dan jinkiri kadan kafin a tabbatar da ketar da Kim Min-woo ya yi wa Viktor Claesson ta hanyar bidiyo, kuma lafiri ya ayyana fenareti, kana Granqvist ya yasar da mai tsaron gida Cho Hyun-woo.

Sweden, wadda ita ma tana saman teburin rukuni na F da maki uku kamar Mexico, ta samu damarmaki masu kyau a Nizhny Novgorod.

Da Marcus Berg ya ci kwallo a tsakiyar wasa kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma Cho ya doke kwalon da ya buga, yayin da Koriya ta Kudu ta kasa auna mai tsaron gidan Sweden ko sau daya.

A wani wasa cike da hayaniya, Cho ya kuma doke wani kwalon da Ola Toivonen bugo da kai.

Koriya ta Kudu a gasar kofin duniyarta ta tara a jere ta kasa katabus kuma damar da ta samu kawai ita ce lokacin da Koo Ja-cheol buga kwallo da kai zuwa gefen raga.

Wannan sakamakon na nufin Mexico, wadda ta yi nasara kan Jamus da ci daya mai ban haushi ranar Lahadi, da kasar Sweden suna da maki uku-uku bayan bayan wasannin farko a rukunin F.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba