Japan ta kafa tarihi a Rasha 2018 bayan doke Colombia

Yuya Osako Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ce kwallo ta uku da Yuya Osako ya ci wa Japan

Yuya Osako ne ya ci wa Japan kwallonta ta biyu da ka domin samun nasara kan Colombia, wacce ta kammala wasan na rukunin G da mutum 10.

Shinji Kagawa ne ya fara zuwa kwallo ta bugun fanareti bayan da Carlos Sanchez ya taba kwallo da hannu, abin da ya sa aka ba shi jan kati.

Colombia ta rama kwallon ta hannun Juan Quintero kafin a tafi hutun rabin lokaci, wanda ya ci kwallon daga bugun tazara.

Sai da aka yi amfani da na'urar tantance kwallo kafin a tabbatar da ita.

Sai dai kwallon da Osako ya ci da ka minti 17 kafin a tashi ta raba-gari tsakanin kasashen biyu a filin wasa na Mordovia Arena.

Wannan nasara ta sa Japan ta zamo kasa ta farko daga nahiyar Asiya da ta doke wata kasa daga Latin Amurka a tarihin gasar cin kofin duniya.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba