Russia 2018: Ronaldo ya kora Maroko gida

Portugal forward Cristiano Ronaldo celebrates scoring against Morocco at the World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Cristiano Ronaldo ya ci gaba da cin kwallo a gasar kofin duniya, inda ya ci kwallo daya tilo da ta bai wa kasarsa damar cire Maroko daga gasar kofin duniya.

Hankali ya koma kan dan wasan na kungiyar Real Madrid a filin wasa na Luzhniki Stadium tun da aka fara wasan, bayan kwallo ukun da ya ci a wasan kasarsa na farko da Spain.

Kuma dan wasan ya ba marada kunya.

Kyaftin din na Portugal ya ci kwallon ne a minti na hudu da fara wasan.

Kwallon ta Ronaldo ta saka zakarun na nahiyar Turai a saman rukunin B, kafin Spain ta kara da Iran ranar Laraba.

Maroko wadda ta rasa samun karbar bakuncin gasar kofin duniya wadda za a yi a shekarar 2026 a makon jiya, ta zama kasa ta biyu da aka cire daga gasar ta kofin duniya bayan kasar Masar.