Anya Messi da Argentina za su kai labari?

Messi Hakkin mallakar hoto EPA

Daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa na duniya na fuskantar kalubalen ficewa daga gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha.

Lionel Messi na Argentina, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyar, zai jagoranci kasarsa a wasa na biyu na rukunin D da za su kara da Croatia.

Za su shiga wannan wasa ne da matsin lamba ganin cewa sun tashi canjaras ne kawai a wasansu na farko da Iceland.

Hakan ya sa Argentina samun maki daya, yayin da Croatia ta doke Najeriya da ci 2-0, abin da ya bata maki uku, kuma ta kasance jagora a rukunin.

Idan har Argentina ta sha kaye a hannun Croatia, kuma Iceland ta samu nasara a kan Najeriya ranar Juma'a, to babu shakka makomarta a gasar za ta kara shiga cikin rashin tabbas.

Messi, wanda ya lashe gasar cin kofin Zarakun Turai sau hudu da Barcelona, da kofunan La Liga da sauran kofuna da dama a matakin kulob, bai taba cin wani muhimmin kofi da tawagar kasarsa ba.

Kuma wasu na ganin wannan ce gasar kofin duniya ta karshe da gwarzon dan kwallon zai taka.

Musamman ganin cewa ya taba sanar da yin ritaya daga bugawa Argentina kwallo a baya, kafin daga bisani ya sauya shawara.

Messi zai so ya nuna kansa kuma ya fitar da kasarsa kunya, musamman ganin yadda ya zubar da fanareti a wasansu da Iceland.

Bugu da kari ganin yadda babban abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ya ke haskakawa a gasar, inda kawo yanzu ya ci kwallo hudu a wasa biyu.

Wasu dai na ganin Messi zai yi kukan-kura a wasan na Croatia domin ceto Argentina daga barazanar da ta ke fuskanta na ficewa daga gasar.

Sai dai a gefe guda wasu na ganin cewa zai yi wuya, kuma ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, musamman ganin yadda ita ma Crotia ba kanwar lasa ba ce.

Wasannin da za a buga a ranar Alhamis

13:00 BST DENMARK v AUSTRALIA

16:00 BST FRANCE v PERU

19:00 BST ARGENTINA v CROATIA