Russia 2018: Mene ne yake damun Lionel Messi?

Will Messi depart Russia 2018 that early thanks to Argentina's abysmal performance so far? Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rashin tabuka abin kirkin Messi a Gasar Cin Kofin Duniya zai iya sa a cire Argentina daga gasar da wuri

Wani hoto da ke nuna dan wasan Argentina Lionel Messi yana fita daga filin wasa bayan Croatia ta doke kasarsa da ci 3-0 a ranar Alhamis, ya kasance wani abin daukar hankali a Gasar Cin Kofin Duniya wanda ake yi a kasar Rasha.

Bayan kasarsa ta buga wasanni biyu a gasar, Messi wanda sau biyar yana zama gwarzon dan kwallon duniya, ya kasa zura kwallo ko da guda a raga - hasalima ya barar da bugun fenareti a wasansa da kasarsa ta yi da kasar Iceland.

Alamu na nuna cewa Argentina za ta iya koma wa gida bayan kammala wasanni rukunin - wato karo na biyu ke nan tun bayan da aka cire ta a irin wannan mataki a gasar a shekarar 2002.

Messi, mai shekara 30 a duniya, zai iya kara halartar Gasar Cin Kofin Duniya da ke tafe. Amma wadansu masu sharhi kan kwallon kafa suna ganin wannan ce dama ta karshe da dan kwallon zai iya cire wa kasarsa kitse a wuta.

Babbar nasarar da dan kwallon ya samu da kasarsa ita ce ta lashe lambar zinare a gasar Olympics wadda aka yi a birnin Beijing a shekarar 2008.

Kazalika dan wasan bai taka wata rawar a-zo-a-gani ba a kungiyarsa ta Barcelona a kakar bana: kodayake kungiyar ta lashe kofin La liga amma kuma an yi waje da ita a wasan gab da na kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai sau uku a jere a kaka uku.

Akwai abubuwa da dama da ake ganin sun jawo wa Messi rashin katabus a wannan kakar. Mun jero su a nan kasa:

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gajiya da rauni suna daya daga cikin abubuwan da ke jawo wa Messi cikas

1) Rashin kuzari

A kakar 2017/18 a nahiyar Turai, Messi ya yi wasanni 54, wannan ne lokacin da ya fi yin wasa tun kakar 2014/15 kuma ma fi yawa a shekara biyar.

Kamar yadda kididdigar shafin Transfermarkt, Messi ya buga wasa har na tsawon mintuna 4,468 kuma ya taka leda har tsawon mintuna 82.7.

Sai dai ya kammala kakar da kwallaye 45 a raga kuma ya taimaka aka ci kwallo sau 18 a Barcelona.

2) Jinyar rauni

A watan Afrilun 2018, wata jaridar Argentina, Clarin, ta ruwaito cewa Messi yana fama da rauni a cinyarsa ta dama kuma hakan yana shafar karsashinsa wajen gudu.

Matsalar ta fito fili ne bayan wasannin sada zumuntar da Argentina ta buga da Italy da Spain.

Messi ya kalli wasan da Spain ta doke su da ci 6-1 ne daga benci.

3) Argentina ba ta wasa kamar yadda aka santa

Argentina ta fuskanci kalubale yayin da take neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya a Rasha, inda ta sha da kyar.

Messi shi ne dan wasan Argentina da ya fi zura kwallo a raga a wasan, inda yake da kwallaye bakwai, amma hakan bai hana magoya baya da kafafen yada labarai caccakar dan kwallon ba.

Kodayake Argentina ta kai wasan karshe na Gasar cin Kofin Duniya wadda aka yi a Brazil, sai dai ta yi rashin nasara a hannun kasar Jamus da ci 1-0 - gasar shekarar 1986 ce ta karshe da Argentina ta dauki kofin duniya.

Tun bayan lashe kofin Copa America a shekarar 1993, Argentina ba ta lashe wani babban kofi ba.

Kuma lambar zinaren da suka lashe a gasar Olympics a shekarar 2004 da 2008 hakan bai magance damuwar ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo ya zura kwallaye hudu a raga a Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Rasha

4) Messi idan aka kwatanta shi da Ronaldo

Rashin katabus din da Messi yake yi ya kara fito fili bayan rawar da abokin hamayyarsa Ronaldo yake takawa a Gasar Cin Kofin Duniya.

Cristiano Ronaldo ya fara Gasar Cin Kofin Duniyar ne da kafar dama, inda ya ci kwallaye uku a wasansu na farko da kasar Spain.

Ronaldo ya kara zura kwallo a raga a wasansu da Maroko wanda aka tashi 1-0.

Abin guda da za a rika tuna Messi da shi ne barar da fenaritin da ya yi a wasansu da Iceland.

Shekara biyu da suka wuce, Ronaldo ya yi abin da Messi ya kasa yi - wato ya jagoranci kasar ta lashe kofin Euro a shekarar 2016.