Ahmed Musa ya fitar da Super Eagles kunya

Ahmed Musa Hakkin mallakar hoto Lars Baron - FIFA
Image caption Ahmed Musa ya yi sujjada domin godiya ga Allah bayan da ya ci kwallon

Kwallo biyun da Ahmed Musa ya zura a minti na 49 da 75 sun bai wa Najeriya damar da doke Iceland da ci 2-0 a gasar kofin duniya.

Wannan nasara ta bai wa Super Eagles damar hada maki uku bayan wasa biyu.

Kuma a yanzu ita ce ta biyu a rukunin bayan Croatia wacce tuni ta kai mataki na gaba bayan da ta doke Argentina da ci 3-0 a ranar Alhamis.

A yanzu Ahmed Musa shi ne dan kwallon da ya fi kowanne ci wa Najeriya kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya, inda ya zura hudu.

Najeriya za ta kara da Argentina a wasan ta karshe na rukunin D domin fayyace kasar da za ta bi Croatia domin zuwa zagayen kifa-daya-kwala 'yan 16.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images