Damben Nuran Mahaukaci da Garkuwan Shagon Alabo
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Nura da Garkuwan Shagon Alabo

Dambe 14 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Ciki har da wasan Nuran Mahaukaci Teacher daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga cikin guda 11 da aka yi canjaras.

Wasannin da aka yi kisa kuwa:

 • Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa ya buge Shagon Dogon Auta daga Kudu a turmin farko
 • Shagon Faya daga Kudu ya yi nasara a kan Dogon Washa Guramada a turmin farko
 • Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya buge Garkuwan Sojan Kyallu Gurumada a turmin farko

Sauran damben da aka yi canjaras:

 • Shagon Sojan Kyallu Guramada da Shagon Shegiyar Mota daga Arewa
 • Dogon Ebola daga Kudu da Bahagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
 • Ali Gangare Guramada da Kadiri daga Arewa
 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Sule Shagon Sama'ila daga Kudu
 • Dan Yalo Autan Sikido daga Kudu da Shagon Bahagon Maimatsala Guramada
 • Bahagon Audu Dan Crespo daga Arewa da Shagon Dogon Bahagon Sisco daga Kudu
 • Garkuwan Reza Bunza Guramada da Dan Yalo Autan Sikido daga Kudu
 • Dogon Sisco daga Kudu da Dila Shagon Reza Guramada
 • Dogon Aleka daga Kudu da Garkuwan Dangero Guramada
 • Sule Shagon Sama'ila daga Kudu da Ali Gangare Guramada

Labarai masu alaka