World Cup 2018: Saudiyya ta doke Masar 2-1

Essam El Hadary (right) Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Golan Masar Essam El Hadary ya ture fanaretin dan wasan Saudiyya Fahad Al Muwallad

Mohamed Salah ya ci kwallonsa ta biyu a gasar kofin duniya amma Masar ta sha kashi a hannun Saudiyya a filin wasa na Volgograd Arena.

Dan wasan na Liverpool ne ya fara zura kwallo bayan da ya daga kwallon saman golan Saudiyya Yasser Al-Mosailem a minti na 22.

Golan Masar Essam El Hadary, wanda ya zamo dan wasa mafi tsufa da ya murza-leda a gasar kofin duniya, ya kabe fanaretin Fahad Al Muwallad.

Sai dai bai iya kabe fanareti na biyu da Salman Al Faraj ya buga, kafin Salem Al Dawsari ya ci ta biyu ana daf da tashi daga wasan.

Duka kasashen biyu dai sun fice daga gasar bayan da suka sha kashi a wasannin biyu na farko.

Sai dai Masar ta tafi gida babu maki ko daya.

A daya wasan da aka buga a rukunin A, Uruguay ta lallasa mai masaukin baki Rasha da ci 3-0.