Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

Dan wasan Najeriya Abdullahi Shehu ya ce ba sa jin tsoron shahararren dan wasan Argentina Lionel Messi gabanin karawarsu a gasar cin kofin duniya a ranar Talata.

Wasan ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar yayin kowace take neman yin nasara.

Ba wannan ba ne karon farko da kasashen suke haduwa a tarihin gasar, sai dai a baya Argentina ce take samun nasara a dukkannin karawa hudu da suka yi a gasar.