Najeriya da Argentina: Fargaba ta sa Maradona ganin likita

Diego Maradona Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Diego Maradona ya halarci dukkan wasannin Argentina a gasar ta bana

Gwarzon dan kwallon Argentina Diego Maradona ya ce "yana cikin koshin lafiya" bayan da likita ya duba shi a lokacin wasan da kasar ta doke Najeriya a gasar kofin duniya a ranar Talata.

Maradona mai shekara 57, wanda ya jagoranci Argentina lashe gasar a shekarar 1986, ya ce "wuyansa ya rinka ciwo sosai".

Ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zmunta da ke nuda yadda likitoci suka duba shi a lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci na wasan da Argentina ta yi nasara da ci 2-1.

Sai dai ya karyata cewa an kai shi asibiti.

"Ina so na gaya wa kowa cewa na samu lafiya," kamar yadda ya fada a shafinsa na Instagram.

"Na ga likita kuma ya bani shawarar na tafi gida kafin a dawo daga hutun rabin lokaci, amma na tsaya saboda muna kan siradi. A don haka ta ya ya zan tafi?"

Nasarar da Argentina ta samu na nufin ta kai zagaye na biyu inda za ta kara da Faransa a ranar Asabar.

Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna kamar Maradona ya kasa tashi daga kan kujerarsa a lokacin da aka kammala wasan, amma BBC ta samu bayanan da ke cewa daga bisani ya hau jirgi domin komawa birnin Moscow.

Da farko an nuno shi ya na kuka lokacin da wasan ya ke 1-1, wanda da an tashi a hakan da an fitar da Argentina daga gasar.

Daga bisani ne kuma bayan Marcos Rojo ya ci musu kwallo ta biyu ana dab da tashi sai aka nuno shi yana daga dan-yatsan shi guda.

Maradona ya buga wa Argentina wasa 91, inda ya ci kwallo 34, sannan kuma daga bisani ya jagoranci tawagar kasar a matsayin koci.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba