Kocin Masar ya yi murabus

Hector Cuper Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin tawagar kwallon Masar, Hector Cuper ya bar aikinsa bayan kasar ta fice daga gasar kofin duniya a matakin rukuni.

Masar, wadda ta samu zuwa gasar kofin duniya a karon farko cikin shekara 28, ta kammala zagayen rukuni a kasan teburin rukunin A.

Kuma ta kasa samun maki ko guda.

Shan kayen da suka yi a hannun Uruguy 1-0 ya zo ne kafin su sha kaye a hannun Rasha da 3-1, san nan kuma Saudiyya ta doke su da 2-1.

Raunin da Mohamed Salah ya ji ya mamaye shirin da Masar ta yi wa gasar kofin duniya.

Kocin mai shekara 62, wanda dan kasar Argentina ne yana gab da karasa kwatiraginsa da kasar ne bayan gasar kofin duniya.

Amma ya fara tattaunawa da hukumar kwallon kafa ta kasar Masar game da kwantiraginsa kafin a fara gasar.

Da yake magana kafin ganawarsa da hukumar kwallon kafar kasar bayan Saudiyya ta doke su, kocin ya ce zai ga abin da zai faru.

Hukumar kwallon kafar ta ce: "Mun gana bayan mun dawo daga Rasha, kuma shugabannin hukumar sun yanke shawarar bayyana godiyarmu ga Cuper da ma'aikatansa musamman ganin yadda ya jagoranci kasar ta je gasar cin kofin duniya bayan shekara 28."