Kofin Duniya: Me ya sa zakara ke shan kashi tun a zagayen farko?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun 2002 ake fitar da kasar da ta lashe kofin duniya a zagayen farko

Ta tabbata an fitar da Jamus a gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha.

Kasar da ta lashe kofin a 2014 ta fice tun a zagayen farko bayan shan kashi 2-0 a hannun Koriya ta kudu.

Jamus ita ce ta karshe a teburin rukunin F; wasa daya kawai ta yi nasara daga wasannin rukuni uku da ta buga, kuma hakan ma da kyar ta ci Sweden 1-0 ana dab da hure wasa minti 95.

Hakan na nufin ta sake faruwa, kamar an yi wa duk kasar da ke rike kofin duniya baki ba za ta kai labari ba.

Tun Faransa 1998 babu kasar da ta kare kofin duniya da ta lashe. Kuma tun a zagayen farko ake fitar da su.

  • Faransa ta ci kofi 1998
  • A 2002 an fitar da Faransa a zagayen farko
  • Italiya ta ci kofi 2006
  • A 2010 an fitar da Italiya a zagayen farko
  • Spain ta ci kofi 2010
  • A 2014 an yi waje da Spain tun a zagayen farko
  • Jamus ta ci kofi a 2014
  • A 2018 tarihi ya maimata kansa an fitar da Jamus tun a zagayen farko

Shin tsinuwa ce ta karni na 21?

Kafin gasar 2002, sau biyu kawai aka taba ganin kasashen da suka lashe gasar suka yi gaggawar ficewa ba shiri. A 1950 tun a zagayen farko aka fitar da Italiya bayan ta lashe kofin a 1946 da kuma Brazil a 1966, lokacin da ta ke kokarin daukar kofin sau uku a jere.

Daga nan sai 2002 da Senegal ta yi waje da Faransa a wasan rukuninsu na farko a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Koriya ta kudu da Japan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamus ce ta lashe gasar cin kofin duniya wadda aka yi a kasar Brazil a shekarar 2014
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mesut Ozil na cikin tawagar ta da lashe gasar a shekara ta 2014 a Brazil

Faransa ta lashe kofin 1998 bayan ta lallasa Brazil 3-0.

Tarihi ya maimaita kansa - Italiya da ta fitar da Faransa a 2006, ta yi gaggawar ficewa tun a zagayen farko a rukuninsu da ya kunshi Paraguay da New Zealand da kum Slovakia.

Bayan shekaru hudu kuma ta sake faruwa da Spain da ta lashe kofin a 2010 a Afirka ta kudu inda ta yi fitar gaggawa tun a zagayen farko a Brazil 2014 bayan Netherlands ta lallasa ta 5-1 sannan Chile ta doke ta 2-0 a wasan rukuni.

A bana kuma tarihi ya sake maimaita kansa inda rukunin da ya kunshi Sweden da Mexico da Koriya ta kudu ya kori Jamus da ta lashe kofin a Brazil 2014.

Jamus ba ta sha da dadi ba a Rasha 2018, inda wasanta na farko ta sha kashi 1-0 a hannun Mexico kuma duk da ta samu sa'ar Sweden 1-0 a wasa na biyu amma kuma Koriya ta Kudu ta kora ta gida bayan ta doke ta 2-0 a wasan karshe na rukuninsu.

Wannan al'amari na fitar da kasar da ke rike da kofin duniya tun a zagayen farko wasu na ganin zai ci gaba da tasiri a nan gaba, saboda yadda wasannin lig ke gajiyar da 'yan wasa.