Javier Mascherano ya yi ritaya daga buga wa Argentina kwallo

Argentina defender Javier Mascherano Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Javier Mascherano ya lashe lambar zinaye ta Olympics a 2004 da 2008 amma bai taba lashe kofin duniya da Argentina ba

Dan wasan tsakiya na Argentina Javier Mascherano ya yi ritaya daga buga wa kasar kwallo bayan da aka fitar da su daga gasar kofin duniya.

Dan kwallon mai shekara 34 ya bugawa kasar wasa sau 145, ciki har da wanda suka sha kashi a hannun Faransa da ci 4-3 a zagayen 'yan 16 a ranar Asabar.

Mascherano ya buga dukkan wasannin da Argentina ta yi a gasar ta Rasha - kuma ita ce ta hudu da ya halatta a jere.

Ya shaida wa DeportTV: "Ni dai a wuri na, komai ya zo karshe. Daga yanzu ni ma magoyin bayan Argentina ne kawai."

Dan kwallon wanda ya lashe lambar zinare ta Olympic sau biyu, ya fara bugawa kasar wasa ne a 2003, kuma ya fara kwallo ne a kulob din River Plate.

Ya buga kwallo a West Ham, Liverpool da kuma Barcelona. A yanzu yana murza-leda ne a China tare da Hebei China Fortune.