Iniesta ya yi ritaya daga buga wa Spain kwallo

Andres Iniesta

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Iniesta, wanda ya fara bugawa kasar kwallo a 2006, ya kuma lashe gasar kasashen Turai a 2008 da 2012

Andres Iniesta, wanda ya zura kwallon da ta bai wa Spain damar lashe gasar kofin duniya a 2010 ya yi ritaya daga buga mata wasa bayan an fitar da su daga gasar Rasha 2018.

Dan kwallon mai shekara 34 an sako shi ne bayan an dawo hutun rabin lokaci a wasan da Spain ta sha kashi a hannun Rasha da ci 4-3 a bugun fanareti a zagayen 'yan 16 ranar Lahadi.

Kwallon karshe da Iniesta ya buga ita ce fanaretin da ya ci a wasan wanda shi ne na 131 da ya buga wa kasar.

"A zahiri ta ke cewa wannan shi ne wasana na karshe a tawagar," a cewarsa.

Iniesta, wanda ya fara bugawa kasar kwallo a 2006, ya kuma lashe gasar kasashen Turai a 2008 da 2012.

"Wani lokacin ba ka samun kyakkyawan karshe kamar yadda ka so. Wannan ita ce ranar da ta fi kowacce muni a rayuwata."

A watan Mayu ne Iniesta ya kawo karshen shekara 22 da ya shafe a Barcelona inda ya koma kulob din Vissel Kobe na kasar Japan.

Ya lashe kofuna 32 a Barcelona, inda ya buga wa babbar tawagar kungiyar wasa 674 bayan da ya fara a karamar tawagar tun yana dan shekara 12.