Mohamed Salah ya amince da kwantiragin shekara 5 a Liverpool

Liverpool forward Mohamed Salah

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Salah ya ci kwallaye 32 a gasar Firimiya a kakar da ta gabata

Dan wasan gaban Liverpool, Mohamed Salah, ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta shekara biyar da kulob din.

Dan wasan dan kasar Masar mai shekara 26, wanda ya koma the Reds kan kudi fam miliyan 34 daga Roma a lokacin bazarar da ta gabata, ya ci kwallaye 44 cikin wasanni 52 da ya buga wa kulob din.

Sabuwar yarjejeniyarsa, wadda za ta kai zuwa shekarar 2023, ba ta kunshi zabin sallama.

"Wannan ya nuna abubuwa biyu karara - imaninsa da Liverpool da kuma imanin kullob din a kansa," in ji kocin Liverpool, Jurgen Klopp.

Salah ne ya fi zura kwallo a raga a gasar Firimiyar bara inda ya ci kwallaye 32 a gasar - lamarin da ya sa ya ci kyautar takalmin zinari.

Irin rawar da ya taka ya kuma sa ya ci kyautar dan kwallon da ya fi iya taka leda ta kungiyar 'yan kwallo da ta 'yan jarida a Ingila.

'Mo Salah mai sadaukar da kai ne'

"Ina tunanin za a iya ganin wannan labarin yadda yake; bayar da lada ga wanda ya yi aiki tukuru tare da bayar da gudumawa ga kungiya da kulob din a kakar badi," in ji Klopp.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Muna son kwararrun 'yan wasa su ga cewar suna da wurin zama a Anfield inda za su iya cimma burinsu na kwallon kafa - muna aiki tare domin cimma wannan.

"A duk lokacin da wani kamar Mo Salah ya sadaukar da kai kuma ya ce wannan ne gidana, ina ganin hakan zai bayyana a fili.

"Bugu da kari, yadda muka rike shi ya nuna cewa mun ga darajarsa kuma muna son ya kara daraja tare da kara kwarewa a kulob dinmu," in ji Klopp.

Liverpool ta karkare ta hudu a teburin gasar Firimiya a kakar da ta wuce, kuma ta kai ga matakin kusa da dab da na karshe a gasar Zakarun Turai, inda ta sha kaye a hannun Real Madrid da ci 3-1.

Dole Salah ya fice daga wasan bayan minti 30 a karawarsu da kungiyar ta Sifaniya bayan da ya ji ciwo a kafadarsa sakamakon 'buge shi' da dan wasan baya na Real Madrid Sergio Ramos ya yi.

Wannan matsalar ta sa an yi tababa game da wasansa a gasar kofin duniya ta shekarar 2018, kuma bai buga wasan farko na kasarsa Masar ba - inda ta sha kaye a hannun Uruguay da ci 1-0 kafin ya buga wasansu da Rasha da kuma Saudi Arebiya.

Salah ya ci kwallaye a wasannin, amma bai iya hana kasarsa shan kaye da kuma ficewa daga gasar a matakin rukuni ba.