'Yan sanda sun yi 'zanga-zanga' a Maiduguri

police Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan sanda sun yi zanga-zanga a gaban ofishin rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke birnin Maidiguri.

Wasu mazauna birnin na Maiduguri sun shaida wa BBC cewar 'yan sandan sun tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a kan titin da ke tsakanin ofishin rundunar 'yan sandan da kwalejin kimiyya da fasaha ta Ramat a birnin.

Rahotanni dai sun ce 'yan sandan sun yi zanga-zangar ne domin rashin biyan su wasu alawus-alawus da aka saba ba su game da yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Sai dai a wata sanarwa da hukumar 'yan sandan Najeriya ta fitar jim kadan bayan da lamarin ya faru, ta ce ba zanga-zanga 'yan sandan suka yi ba.

A sanarwar kakakin 'yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood, ya ce: "Wasu 'yan sandan kwantar da tarzoma da ke aiki na musamman a Maiduguri sun je ofishin rundunar 'yan sandan jihar Borno game da jinkirin da aka samu wajen biyansu alawus na aiki na musamman da sanyin safiyar Litinin."

"A lokacin da suka fara zanga-zangar, sun yi ta harbi sama," in ji wasu mazauna garin.

Wasu kafafen watsa labarai sun ruwaito cewar rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana sane da matsalar kuma tana kokarin shawo kanta.

Ba kasafai 'yan sanda da kuma sauran jami'an tsaro ke zanga-zanga ba a Najeriya.


Hukumar 'yan sanda ta musanta labarin

Sai dai kuma hedikwatar hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta ba su yi zanga-zanga kan rashin biyansu alawus ba a birnin Maiduguri.

Sanarwar da kakakin hukumar, Jimoh Moshood, ya fitar ta ce ba su je wurin domin yin zanga-zanga kamar yadda aka yi ta yayatawa a shafukan sada zumunta ba.

Moshood ya ce nan take ne Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotum, ya umarci kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi wa 'yan sandan jawabi game da dalilin da ya sa aka samu jinkiri a biyan nasu.

Sufeto Janar din ya kuma ya ce kwamishinan ya ba su tabbacin cewar tun da dai an amince da kasafin kudi za a biya su kudin ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta ce bayan wannan bayanin sun koma bakin aikinsu.

Har wa yau sanarwar ta ce Mista Kpotum ya umarci kwamishinan 'yan sandan kwantar da tarzoma ya tafi jihar Borno da sauran jihohin da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda 'yan sandan kwantar da tarzoma ke aiki na musamman domin fadakar da su game da aikin da ake yi don tabbatar da cewa ana biyan 'yan sandan da ake aiki a yankin alawus-alawus dinsu a kan lokaci.

Hukumar 'yan sandan Najeriyar ta kara da cewar jami'an 'yan sandan kwantar da tarzomar da suka je tambayar ba sa cikin masu aiki da rundunar Operation Lafiya Dole, a yakin da ake da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin Najeriya.

Ta kara da cewa an tura 'yan sandan birnin Maiduguri ne domin hana aikata laifi da sauran ayyukan 'yan sanda a jihar.

Labarai masu alaka