Kotu ta sake ba da umarnin sakin Sambo Dasuki

Dasuki

Asalin hoton, Getty Images

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin a saki tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, kamar yadda lauyansa Ahmed Raji ya tabbarwa BBC.

Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ce ta bayar da belin Dasuki, wanda aka kama shi a ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2015, a wata karar da ya kai kan kare hakkinsa na dan Adam.

Dasuki, wanda a baya kotun tarayyar ta bayar da belinsa sau hudu ban da belinsa da kotun ECOWAS ta bayar, ya nemi kotun ta tilasta wa gwamnatin tarayya ta bi dukkan umarnin kotun da aka bayar na sakinsa.

Lauyansa ya ce a ranar Talata ne za su fara nazari kan sharuddan da kotun ta gindaya musu don fara kokarin ganin sun cika su.

Zuwa yanzu dai babu tabbas kan ko gwamnatin kasar za ta amince da sakin nasa ko kuma za ta bukaci a ci gaba da tsare shi.

Gwamnatin dai ta dade tana cewa tana ci gaba da rike shi ne saboda ta daukaka kara.

Da take yanke hukunci kan karar da lauyan Dasuki, Ahmed Raji, ya shigar, mai shari'a Ijeoma ta ce a saki Dasuki idan ya bayar da naira miliyan 200 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

Kotun ta ce dole mutanen su kasance ma'aikatan gwamnatin tarayya wadanda matakin aikinsu bai gaza mataki na 16 ba, kuma dole ma'aikatan su mika takardar kama aikinsu da kuma wasikar karin girmansu na baya-bayan nan ga kotu kafin a saki Dasuki.

Idan kuma mutum mai zaman kansa ne zai tsaya wa Dasuki, kotun ta ce dole mutumin ya kasance yana da gida a Abuja, kuma dole ya mika takardun gidan ga kotun tare da rantsuwa game da yadda ya same su.

Hakazalika mai shari'ar ta ce dole mutumin ya ajiye naira miliyan 100 a hannun magatakardan kotun, inda za a mayar wa mutumin kudin bayan an gama shari'ar Dasuki.

Mai shari'a Ijeoma ta kuma ce dole wanda zai tsaya wa Dasukin ya mika hotonsa na baya-bayan nan, kuma dole jami'an kotun su tabbatar da adireshinsa a matsayin wani sharadi na bayar da belinsa.

An kama Dasuki ne dai bisa zargin sama da fadi da kudin da aka ware domin sayen makaman yaki da 'yan Boko Haram.