Brazil ta kora Mexico gida

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Neymar ya zura kwallo daya sannan ya taimaka aka shirya daya a wasan da Brazil ya doke Mexico da ci 2-0 a zagayen 'yan 16 na gasar cin kofin duniya.

Mexico sun mamaye zagayen farko na wasan, amma ba su yi amfani da damarmakinsu ba.

Daga bisani ne kuma Brazil suka yunkuro, inda Neymar ya taka rawar gani.

Roberto Firmino ne ya zura kwallo ta biyu ana dab a tashi bayan golan Mexico ya kabe kwallon da Neymar ya buga.

Wannan sakamoko na nufin Mexico ta sake komawa gida a wannan zagayen kamar yadda ta yi a dukkan gasar kofin duniya da ta halatta tun daga shekarar 1994.

A yanzu Brazil za ta kara kasar da ta yi nasara tsakanin Belgium da Japan.

Wannan ne karo na bakwai a jere da Brazil ke kaiwa zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya.