Ingila ta cire Colombia daga Russia 2018

Ingila Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasar Ingila ta tsallake zuwa matakin gab da na kusa da karshe bayan ta doke Colombia 4-3 a bugun fanareti.

Harry Kane ne ya fara zura kallo a ragar Colombia a minti na 57, kafin Yerry Mina ya farke kwallon a cikin minti uku na karin lokaci, abin da ya sa aka tashi wasan kunnen doki 1-1.

Eric Dier ne ya ci wa Ingila kwallo ta hudu a bugun fanareti da ya ba ta damar doke Colombia.

Yanzu Ingila za ta kara ne da kasar Sweden a ranar Asabar domin neman kasar da za ta kai wasan kusa da na karshe a gasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Karanta wadansu karin labarai