Real Madrid na shirin sayar da Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo with the Champions League trophy Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau biyar Ronaldo yana lashe Kofin Zakarun Turai

Kungiyar Real Madrid tana duba yiwuwar sayar da Cristiano Ronaldo ga kulob din Juventus a kan kudi fam miliyan 88.

Dan wasan na Portugal mai shekara 33, ya ci wa Madrid kwallaye 451.

Madrid ta kammala gasar La Ligar bara ne a matsayi na uku, inda abokiyar hamayyarta Barcelona ta lashe gasar.

Ronaldo ya lashe Kofin Zakarun Turai karo na biyar tare da kungiyar Madrid a watan Mayun da ya gabata.

Bayan wannan nasarar ne kocin kungiyar Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa kuma aka maye gurbinsa da tsohon kocin kasar Spain Julen Lopetegui.

Akwai wadanda suke ganin shekarun suna daya daga cikin dalilan da ya sa kungiyar take son rabuwa da dan wasan.

Dan kwallon ya koma Madrid ne daga kungiyar Manchester United a shekarar 2009 a kan fam miliyan 80.

A ranar Laraba wasu rahotanni sun ce Real Madrid da kungiyar PSG sun cimma wata yarjejeniya kan matashin dan wasan Faransa, Kylian Mbappe. wanda ake ganin watakila shi ne zai maye gurbin Ronaldo.

Sai dai Madrid ta musanta labarin zawarcin Mbappe.

Labarai masu alaka