Ya dace Najeriya ta koyi wasan a mutu, ko a yi rai – Balogun

Dan wasan Najeriya Leon Balogun Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Leon Balogun ya buga dukkanin wasannin Najeriya uku a Rasha

Dan wasan baya na Najeriya Leon Balogon ya ce 'yan wasan Super Eagles na bukatar su koyi wasan a mutu ko a yi rai bayan ficewarsu daga Rasha.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta fice gasar cin kofin duniya bayan Argentina ta doke ta a wasan karshe na rukuninsu.

"Yana da muhimmanci wani lokaci a wasan duniya a buga wasan ko a mutu," kamar yadda dan wasan na baya mai shekaru 30 ya shaida wa BBC.

Ya ce abin da Argentina ta yi amfani da shi ke nan, kuma ya kamata wannan ya zama darasi ga 'yan wasan Najeriya domin sai an jajirce idan ana bukatar nasara.

Balogon wanda ya buga wa Najeriya wasanni 22, yana cikin kwararrun 'yan wasa daga cikin tawagar matasan da Najeriya ta tafi da su a Rasha.

Najeriya ta kare ne a matsayi na uku a teburin rukunin D da maki uku bayan ta doke Iceland da ci 2-0.

Kwallon da Marcos Rojo ya ci wa Argentina a ragar Najeriya ana saura minti hudu a tashi wasa ne ya fitar da Super Eagles.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi ya taimakawa Argentina doke Najeriya

Balogon wanda ya buga dukkanin wasannin Najeriya a Rasha ya ce yana fatan kalubalen da suka fuskanta zai kasance alheri ga Super Eagles a nan gaba.

Yawancin 'yan wasan Super Eagles da suka tafi Rasha matasa ne, biyar daga cikinsu ne kawai suka taba buga gasar cin kofin duniya da suka hada da John Obi Mikel da Victor Moses da Ahmed Musa da Echiejile da Oganyi Onazi.