Najeriya za ta kai karar lafari wajen FIFA

Dalung Hakkin mallakar hoto .
Image caption Ministan ya ce ba a yi wa Najeriya adalci ba a gasar

Ministan wasannin Najeriya, Solomon Dalung, ya ce ya umarci hukumar kwallon kafa ta kasar (NFF), da ta shigar da koke gaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, kan yadda ya ce aka yi wa kasar rashin adalci a gasar kofin duniya a Rasha.

Mista Dalung ya ce rashin adalci daga bangaren alkalan wasa ne musabbabin rashin nasarar 'yan wasan kasar a wasanni da suka buga da kasashen Croatia da Argentina.

Ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron abin da ya shaida wa Haruna Shehu Tangaza:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ba a yi wa Najeriya adalci ba a gasar kwallon duniya — Dalung

Bana ne dai aka fara amfani da na'urar bidiyo wajen taimaka wa alkalin wasa domin yanke hunkunci a kan wasu abubuwan da suka faru a kan fili ba tare da ya gani ba.

Wasu 'yan Najeriya ba su ji dadin yadda alkalin wasan Najeriya da Argentina ya ki bayar da fanareti ba duk da cewa bidiyo ya nuna yadda kwallo ta taba hannun dan wasan Argentina.

Sai dai kuma wasu suna ganin hukuncin da lafarin ya yanke ya yi daidai.

Labarai masu alaka