Kofin Duniya: Ingila ta kai zagayen dab da karshe

Bayanan bidiyo,

Yadda Ingila ta doke Sweden

Ingila ta kai zagayen dab da karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha bayan ta doke Sweden 2-0.

Harry Maguire da Dele Alli ne suka ci wa Ingila kwallayen a ragar Sweden.

Karon farko ke nan da Ingila ta tsallake zuwa zagayen dab da karshe a gasar cin kofin duniya tun Italiya 1990.

Yanzu Ingila za ta hadu ne da da Rasha ko Croatia a ranar Laraba a fafatawar zagayen dab da karshe.

Karon farko ke nan a tarihi da kasashen Turai guda hudu za su buga wasan dab da karshe, bayan Faransa da Belgiujm da Ingila sun tsallake a yayin da Rasha ko Croatia ke kan hanya.

Hakan na nufin tsakanin wadannan kasashen na Turai ne dayansu zai lashe kofin gasar.