Luis Enrique ya zama sabon kocin Spain

Luis Enrique Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Luis Enrique ya horas da Barcelona daga 2014 zuwa 2017 sannan ya yi aiki a Roma da Celta Vigo

An nada tsohon kocin Barcelona Luis Enrique a matsayin sabon kocin Spain inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu.

Kocin mai shekara 48 ya maye gurbin Fernando Hierro, wanda ya sauka daga mukamin kocin na wucin-gadi a ranar Lahadi.

Hierro - wanda ba zai koma mukaminsa na daraktan wasanni na kasar ba - an nada shi ne na wucin-gadi bayan da aka kori Julen Lopetegui ana dab da fara gasar kofin duniya.

Enrique ba ya aiki tun bayan lokacin da ya bar Nou Camp a watan Yunin bara.

Enrique, wanda ya taba taka leda a Real Madrid da Barcelona, ya lashe gasar La Liga, da Spanish Cup da kuma zakarun Turai a jere a lokacin yana kocin Barca a 2015.

Wasansa na farko shi ne na gasar Uefa Nations League da su ka buga da Ingila a Wembley a ranar 8 ga watan Satumba.

Spain ta kuma nada Jose Francisco Molina, tsohon golan kasar, a matsayin sabon daraktan wasanni.