Chelsea da Man City na takara, dan Najeriya zai koma Liverpool

Jorginho Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea tana kokarin kayar da Manchester City wajen sayen dan wasan tsakiyar Napoli, dan asalin kasar Italiya, Jorginho, mai shekara 26, in ji Manchester Evening News.

City ta kuma yi tambaya game da dan wasan tsakiyar Real Madrid da Croatia, Mateo Kovacic, mai shekara 24, a lokacin da ake shakka game da zawarcin Jorginho da suke yi, a cewar Mirror.

Kocin Arsenal, Unai Emery, ya yi magana da dan wasan tsakiyar Lorient dan asalin kasar Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 19, domin ya koma Gunners maimakon Paris St-Germain ko kuma Borussia Dortmund, in ji L'Equipe - via Metro.

Da alama dan wasan gaban Bayern Munich dan asalin kasar Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 29, ya shirya domin cigaba da tsayawa a kulob din duk da cewa ana alakanta shi da barin kungiyar, a cewar Bild.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Da alama za a kayar da Chelsea da Tottenham da Manchester City da Barcelona da kuma Inter Milan a wajen sayen dan wasan Najeriya mai shekara 20, Taiwo Awoniyi, wanda ya shirya domin rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da Liverpool wadda ka iya sa ya je buga wasan aro a Monaco, in ji Teamtalk.

Daraktan wasannin Roma, Monchi ya ce zai yi tunani game da tayi a kan mai tsaron gidan Brazil Alisson, amma babu wani kulob din da ya taya dan wasan mai shekara 25, a cewar FourFourTwo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Galatasaray tana kan tattaunawa domin daukar aron dan wasan Everton dan asalin Najeriya, Henry Onyekuru, mai shekara 21, in ji Liverpool Echo.

Tsohon dan wasan gaban Liverpool da Manchester City, Mario Balotelli, zai zama dan wasan da aka fi biya a Marseille a lokacin da ya kammala komawa kulob din daga Nice a cikin 'yan kwanakin nan, a cewar RMC - via Talksport.

Dan wasan gaban Chelsea dan asalin kasar Belgium, Eden Hazard, mai shekara 27, ya ce Real Madrid "na sa kowa ya yi mafarki" duk da cewa kulob din ba ya hannun Zinedine Zidane, in ji jaridar Marca ta Spain.

Labarai masu alaka