Riyad Mahrez ya koma Man City

Riyad Mahrez Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Manchester City ta sayi dan wasan Leicester City Riyad Mahrez a kan fam miliyan 60.

Dan kwallon mai shekara 27 shi ne dan wasan farko da City ta saya tun bayan lashe Gasar Firimiya ta bana.

Tun a watan Janairun City ta so sayen dan wasan, amma sai cinikin bai kammalu ba.

Mahrez, wanda dan kasar Aljeriya ne, ya koma Leicester City ne daga kungiyar Le Havre a kan fam 400,000 a shekarar 2014.

Ya ci wa Leicester kwallaye 48 a wasanni 179 da ya taka mata leda.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka