'Hazard zai maye gurbin Ronaldo, Liverpool na son Dybala', wa Man U za ta saya?

Paulo Dybala
Bayanan hoto,

Paulo Dybala na taka rawa sosai a Juventus

Tsohon kocin Ingila da Real Madrid Fabio Capello ya ce komawar Ronaldo zuwa Juventus "wata babbar bajinta ce". Kocin dan Italiya a yanzu yana hasashen dan wasan gaba na Argentine Gonzalo Higuain, mai shekara 30, ya koma Chelsea, a cewar (Football Italia).

Dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard, mai shekara 27, shi ne wanda ake hasashen zai maye gurbin Ronaldo a Real Madrid - kuma dan kwallon na Belgium zai bar Stamford Bridge idan dai ba wata damar ya samu da ta fi wannan ba, in ji (Football London).

Ana tunanin zuwan Ronaldo zai sa Juventus ta sayar da wasu 'yan wasanta domin cimma tsarin Uefa na kashe kudade a kan ka'ida - kuma ana ganin Stefano Sturaro, zai iya komawa Newcastle ko Wolves, kamar yadda (Birmingham Mail) ta rawaito.

Ko Dybala zai koma Liverpool?

A shirye Liverpool take ta zuba fan miliyan 80 domin taya dan wasan Argentina Paulo Dybala, mai shekara 24, a cewar TyC Sportso.

Har ila yau Liverpool ta fara tattaunawa da Stoke domin sayen dan wasan Switzerland Xherdan Shaqiri, wanda yarjejeniyarsa ta ce sai an biya fan miliyan 13 kafin a sayar da shi, in ji (Telegraph).

Manchester United na fuskantar kalubale daga Juventus a yunkurinta na sayen Erling Haaland, dan kasar Norway mai shekara 17 daga Molde FK, a cewar (Mirror).

Bayanan hoto,

Matashin dan kwallo Erling Haaland da Manchester United take nema

Haka kuma jaridar (Sun) ta rawaito cewa kungiyoyi da dama na neman dan wasan baya na Manchester United Victor Lindelof, mai shekara 23, a matsayin aro saboda rawar da ya taka a gasar kofin duniya da Sweden.

Rahotanni daga Jamus na bayyana cewa Robert Lewandowski na son barin Bayern Munich, inda Real Madrid ke daya daga cikin kungiyoyin da zai iya komawa.

Dan wasan da Arsenal take nema Gelson Martins, mai shekara 23, na daf da komawa Atletico Madrid. Ana sa ran dan kwallon na Portugal, wanda kwantiraginsa ta kare, zai kammala komawa Madrid a wannan makon.

Akwai yiwuwar Arsenal za ta rabu da mai tsaron gida David Ospina, zuwa Boca Juniors, inda ake sa ran zai kammala komawa kungiyar kam fan miliyan 6, a cewar (Mirror).

Tottenham da Roma sun matsa kaimi a yunkurinsu na sayen dan kwallon Brazil Malcom, mai shekara 21, kamar yadda jaridar (France Football - in French)ta rawaito.