Ma'aikatan Italiya na yajin aiki kan cinikin Ronaldo

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AFP

Ma'aikata a wata masana'antar Chrysler a kamfanin Fiat a kasar Italiya suna yajin aiki bayan mutumin da ya fi hannun jari a kamfanin ya yanke shawarar kashe fam miliyan 99 wajen sayen Cristiano Ronaldo daga Real Madrid.

Iyalan Allegri ne suka mallaki Juventus da kuma kamfanin motocin duka.

Ga ma'aikatan kamfanin, matakin sayen dan wasan na nufin kamfanin Fiat ya rasa jarin da ya kamata a saka masa.

Kungiyar ma'aikatan ta ce kamfanin na bukatar tabbatar da makomar dubban mutane, "maimakon azurta mutum daya tilo".

Kungiyar ta kara da cewa bai "kamata a kashe miliyoyin kudaden Yuro wajen sayen dan wasa daya ba."

A ranar Talata ne Madrid da Juventus suka amince kan cinikin dan kwallon mai shekara 33 a kan fan miliyan 99.2, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da zakarun na Italiya.

Hakan na nufin zai zamo daya daga cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.

Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid

Labarai masu alaka