Chelsea ta kori Antonio Conte

Antonio Conte

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea ta kasa samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai a bana

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sallami kocinta Antonio Conte bayan ya shafe shekara biyu yana jan ragamar kungiyar.

An kore shi ne shekara guda kafin cikar wa'adin kwantigarinsa na shekara uku.

Conte ya lashe Kofin Firimiya a kakar bara da kuma kofin FA a watan Mayu da ya wuce, sai dai Chelsea ta kammala kakar firimiyar bana ne a matsayi ta biyar - wato hakan yana nufin ba za ta shiga Gasar Zakarun Turai ba ke nan.

Akwai rahotanni da ke cewa tsohon kocin kungiyar Napoli Maurizio Sarri ne zai maye gurbin Conte.

Idan aka nada Sarri, zai zama kocin Chelsea mai cikakken iko na tara tun bayan Roman Abramovich ya sayi kulob din a shekarar 2003.