Madrid za ta sayi Hazard fam 150m, Barca na neman Willian

Willian

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid na shirin sayen dan wasan gaban Belgium Eden Hazard, mai shekara 27, kan kudi fam miliyan 150 daga Chelsea a wannan lokacin bazarar domin ya maye gurbin Cristiano Ronaldo, wanda ya koma Juventus, in jiMail.

Tottenham ta shirya domin sayar da dan wasan kasar Belgium, mai shekara 29, Toby Alderweireld, kafin a fara sabuwar kakar gasar Firimiya kuma za ta yi nazari a kan wata yarjejeniya da Manchester United, in ji Yahoo Sport.

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United tana zawarcin Gareth Bale, mai shekara 28, kuma za ta tattauna da sabon kocin Real Madrid, Julen Lopetegui, yayin da dan wasan gaban Wales din yake kokarin tantance makomarsa, a cewar Sky Sports.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya yanke shawarar cewa shi ba zai sayi wani sabon mai tsaron gida ba a wannan lokacin bazarar, in ji Mirror.

Chelsea ta samu tayi na biyu da ya kai fam miliyan 60 daga Barcelona kan dan wasan Brazil, Willian, mai shekara 29, in ji Mail.

Dan wasan gaban kulob din DC United, Wayne Rooney, mai shekara 32, ya ce Everton "ta bayyana karara " cewar tana son ya bar kulob din a wannan lokacin bazarar, shi ya sa tsohon keftin din Ingilan ya koma taka leda a kulob din na Amurka, in ji ESPN

Arsenal da Chelsea ka iya rasa dan wasan tsakiyar CSKA Moscow da Rasha, Aleksandr Golovin, domin dan wasan mai shekara 22 ya fi son komawa Juventus, in ji Tuttosport

Manchester United tana shirin sayen dan wasan Leicester City, Harry Maguire, mai shekara 25, amma suna fuskantar yanayin da zai sa su biya fan miliyan 50 kan dan kasar Ingila din , in ji Mail

Liverpool ta taya dan wasan Besiktas da Croatia, Domagoj Vida, mai shekara 29, kan kudi fan miliyan 17.7, in ji Fanatik