Wa zai lashe kofin duniya tsakanin Faransa da Croatia?

Fraransa da Croatia Hakkin mallakar hoto FIFA

A ranar Lahadi ne Faransa za ta kara da Croatia a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a Rasha 2018.

Za a buga wasan ne a filin Luzhniki da ke birnin Moscow, kuma duk kasar da ta lashe kofin gasar ta zama zakaran duniya.

Kasar Croatia wacce sau biyar tana zuwa gasar ba ta taba kai wa mataki na karshe ba sai a wannan karon.

Ta shiga gasar a shekarar 1998 da 2002 da 2006 da 2014 da kuma 2018.

A Faransa 1998 ne, Croatia ta zo a matsayin na uku a gasar, mataki mafi girma da ta taba kai wa kafin Rasha 2018 inda za ta iya lashe kofin ko ta zo a matsayi na biyu.

A 1998, Faransa da ta karbi bakuncin gasar ce ta dauki kofin na duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Faransa, Didier Deschamps, na harin lashe kofin a matsayin dan wasa da kuma koci, wanda shi ne kaftin din Faransa a shekarar 1998.

Kuma 1998 ne karon farko da Faransa ta lashe kofin gasar zuwa yanzu, amma ta kai zagayen karshe a 2006 inda Italiya ta lashe kofin a Jamus.

Faransa ta samu shiga gasar kofin duniya sau 14 a tarihi, kuma gasar 2018 ce karo na uku da ta samu ta zo matakin wasan karshe na gasar.

Tarihin fafatawar kasashen biyu

Ranar 8 ga watan Yulin shekarar 1998 ne kasashen suka fara haduwa a fagen tamaula. Faransa ce ta doke Croatia da 2-1.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sun hadu a wasan sada zumunci da suka buga a ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar 1999 , kuma Faransa ce ta lallasa Croatia da ci 3-0.

Sun sake karawa a wani wasan sada zumunci a ranar 28 ga watan Mayu na shekarar 2000, kuma Faransa e ta sake samun nasara a kan Croatia da 2-0.

Karawarsu ta farko a gasar cin kofin Turai a ranar 17 ga watan Yunin 2004 kasashen sun tashi canjaras 2-2.

Sun sake tashi canjaras 0-0 a wani wasan sada zumunci da suka yi ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2011.

A haduwar kasashen biyu a baya, Faransa ta samu galaba kan Croatia sau uku, kuma kasashen sun yi canjaras sau biyu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kylian Mbappe na Faransa ka iya zama dan kasa da shekara 20 da biyu da zai ci kwallo a wani wasan karshe na gasar kofin duniya, bayan kwallon da Pele ya ci a shekarar 1958

Wa zai dauki kofin duniya?

Karawar kasashen biyu dai kamar "Mace ce mai ciki - ba a san me za ta haifa ba"

Kasashen biyu sun fitar da manyan kasashe a gasar har suka kawo mataki na karshe.

Faransa ta fitar da Belgium da Brazil, yayin da kuma Croatia ta fitar da Ingila da Rasha da ke karbar bakuncin gasar, kuma kafin nan ta doke Argentina.

Ba za a iya tabbatar da kasar da za ta dauki kofin ba har sai kasashen biyu sun fafata a minti 90 ko 120 idan gumurzun da za su yi ya kai ga shiga karin lokaci.

Idan aka yi laka'ari da irin nasarorin da kasashen suka samu a tarihin gasar kofin duniya a baya, wasu na daura nasara a kan Faransa.

Sai dai kuma Croatia da ba ta taba wuce matakin dab da na karshe ba a tarihin gasar amma ta doke Ingila da ta taba lashe kofin a baya.

Wasu masana kwallon kafa na ganin duk da cewa tarihi yana da muhimmanci a kwallon kafa amma duniyar tamaula na sauyawa.