Maurizio Sarri ya zama kocin Chelsea bayan Antonio Conte

Maurizio Sarri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Maurizio ya jagoranci Napolizuwa matsayi na biyu a gasar Serie A cikin kakar da ta gabata

Maurizio Sarri ya ce yana son ya kawo "kwallo mai kayatarwa" bayan ya zama kocin kulob din a wata yarjejeniyar shekara uku.

Dan wasan mai shekara 59 zai maye gurbin wani dan kasar Italiya Antonio Conte, wanda aka kora ranar Juma'a bayan ya yi shekara biyu a Stamford Bridge.

Sarri ne ya jagoranci Napoli zuwa mataki na biyu a gasar Serie A a shekaru biyu cikin ukun da ya yi a kulob din, kuma cikin watan Mayu ne aka ayyana Carlo Ancelotti a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sarri ya ce "wannan wani lokaci ne mai cike da farin ciki a tarihin aikina."

"Ina fatan za mu iya gabatar da kwallo mai kayatarwa ga masu goyon bayanmu, kuma ina fatan za mu rinka shiga gasar cin kofi daban-daban a karshen kaka, wanda shi ne abin da ya kamaci wannan kulob din."

Shi ne koci na 13 da mai kulob din Blues, Roman Abramovich, ya nada tun da ya sayi kulob din a shekarar 2003.

Cikin wadanda ya nada kocin akwai Jose Mourinho da Guus Hiddink da aka nada a lokuta biyu.

Wane ne Sarri?

Masani akan kwallon kafar Italiya, James Horncastle

Sarri bai taba wani abin a-zo-a-gani ba a lokacin da yake taka leda, kuma tunda ya kasa aiki a matsayin dan wasan kwallon kafa , ya yi aiki a matsayin dan canji a Banca Toscana.

Ya yi aiki da bangaren kasashen waje na ma'aikatar ne, aikin da ke da alaka da tafiye-tafiye na kasuwanci zuwa cibiyoyin tattalin arzikin Turai, ciki har da birnin Landan -amma wannan aikin bai taba jan hankalinsa kamar kwallon kafa ba.

Yana horas da 'yan wasa a gefe a lokacin, ya bar garin Tuscan zuwa wani garin, kuma a shekarar 2001, a lokacin da amfanin 'yan canji kamar sa ya ragu sosai a gun bankuna yayin da Italiya ke kokarin fara amfanin da kudin euro, Sarri ya yanke shawarar barin aikinsa inda yake samun kudi mai yawa, zuwa ga abin da ya bayyana da cewa "shi kadai ne aikin da zan iya yi a kyauta".

Mene ne ya yi a Napoli?

Image caption Irin nasarar da Maurizio Sarri ya samu a gasar Serie A a kungiyar Napoli

Juventus ta dade tana iko da gasar lig ta Italiya- inda ta ci gasar sau bakwai a jere- amma babu wata kungiya da ta zo kusa da ita a wannan lokacin fiye da Napoli, wanda ta ke bayan Juventus din da maki hudu bayan kakar gasar ta bara.

Sarri ya zo Napoli a matsayinsa na koci mai sa kulob dinsa kai hare-hare, inda kwallaye 94 da Napoli ta ci a kakar 2016-17 ya zama mafi yawa da aka ci a cikin kaka daya tun da aka fara wannan karnin.

A cikin shekaru ukun da ya yi yana jagorantar kulob din , Napoli ta ci kwallaye 251 a gasar Seria A - fiye da ko wace kungiya a gasar.

Shi ne koci dan asalin Italiya da zai jagoranci Chelsea tun lokacin Gianluca Vialli a shekarar 1998, bayan Claudio Ranieri da Ancelotti da Roberto di Matteo da kuma Conte.

Duka da cewa ya yi nasara a cikin gida, ya kasa sa Napoli ta wuce matakin kungiyoyi 16 a gasar Zakarun Turai, a kakar da ta gabata kulob dinsa ne ya zo na uku bayan Manchester City da Shakhtar Donetsk a matakin rukuni na gasar.

Ya koma Napoli ne a shekarar 2015 bayan ya kai Empoli babbar gasar lig din Italiya. Chelsea ce kasar da zai fara horaswa a ketare, kuma bai taba cin wani muhimmin kofi ba.

Hakkin mallakar hoto Twitter

Labarai masu alaka