Ingila ta zama ta hudu bayan Belgium ta doke ta a gasar kofin duniya

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hazard na da hannu a kwallaye biyar cikin wasannin gasar kofin duniya shida a wannan gasar

Ingila ta sha kaye a hannun Belgium a wasan tantance na uku a gasar kofin duniya da suka yi a birnin St Petersburg.

Tawagar Ingila da koci Gareth Southgate ya jagoranta ta taka rawar da Three Lions ba ta taba takawa ba tun shekarar 1990, amma ta kammala gasar da shan-kaye biyu a jere ciki har da kayen da ta sha a hannun Croati a wasan dab da na karshe a gasar.

Belgium ta kasa zuwa wasan karshe na gasar kofin duniya a lokacin farko a lokacin da Faransa ta doke ta.

Thomas Meunier ne ya ci wa Belgium kwallo na farko a wasan na ranar Asabar bayan minti hudu kawai.

Keftin din Belgium Eden Hazard ya taka rawar gani a wasan, kuma shi ne ya ci wa kasarsa kwallo na biyu cikin minti bakwai kafin a gama wasan.