Kafata kafar Hazard – Courtois, Liverpool na neman gola

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Eden Hazard ya taka rawa sosai a tawagar Belgium a gasar kofin duniya da aka kammala a Rasha

Real Madrid za ta biya fan miliyan 200 idan har tana so Chelsea ta sayar mata da dan wasan Belgium Eden Hazard, mai shekara 27, a cewar Times .

Rahotanni sun ce Madrid na son sayen Hazard domin ya maye gurbin Cristiano Ronaldo wanda ya koma Juventus a makon da ya gabata.

Golan Chelsea da Belgium Thibaut Courtois ya ce sabon kwantiragin da aka yi masa tayi "bai yi daidai" da wanda aka yi masa a wani wurin ba.

Ana dai alakanta golan, mai shekara 26, dakungiyar Real Madrid, in ji Daily Mirror.

Courtois ya ce game da abokin wasansa a Chelsea da Belgium Eden Hazard: "Duk inda na je, to kafata kafar Hazard," kamar yadda (Evening Standard) ta ruwaito.

Chelsea na da sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Lazio Sergej Milinkovic-Savic.

Ana kuma alakanta dan kwallon mai shekara 23 da yiwuwar komawa Manchester United, in ji Corriere dello Sport, ta hannun Talksport.

Hakkin mallakar hoto A
Image caption Dan wasan da Manchester United da Chelsea suke rububi

Liverpool ta taya golan Barcelona kuma dan kasar Holland Jasper Cillessen, mai shekara 29, a cewar Mundo Deportivo, ta hannun Talksport.

Kocin kungiyar Jorgen Klopp na bukatar sabon gola domin kara karfin kungiyar a lokacin da ake shirin fara sabuwar kakar wasanni.

A shirye dan wasan Ingila Luke Shaw, mai shekara 23, zai bar Manchester United a lokacin da kwantiraginsa za ta kare, idan har bai samu gurbi na dindin a tawagar Jose Mourinho ba a bana, in ji jaridar (Manchester Evening News).

Everton daTottenham da kuma Chelsea na neman dan wasan tsakiya na Boca Juniors kuma dan kasar Colombia Wilmar Barrios, mai shekara 24, a cewar TyC Sport, ta hannun HITC.

Shugaban kulob din Lyon Jean-Michel Aulas ya ce a shirye yake domin saurarar sabon tayi daga Liverpool kan dan kwallon gaba na kulob din Nabil Fekir, in ji Le10 Sport, ta hannun Liverpool Echo.

Labarai masu alaka