Sa'anni na Qatar da China suke komawa – Ronaldo

Cristiano Ronaldo
Bayanan hoto,

Dubban jama'a ne suka taru domin shaida bikin gabatar da Cristiano Ronaldo a matsayin sabon dan wasan Juventus

Cristiano Ronaldo ya ce yawancin sa'anninsa kan koma Qatar ko China da taka leda saboda shekarunsu sun ja.

Dan kwallon, mai shekara 33, na magana ne jim kadan bayan da aka gabatar da shi a matsayin sabon dan wasan Juventus.

Ya ce "shekaru na 33, ba 23 ba, a don haka in amatukar godiya da Juventus ta bani wannan damar.

"Yawancin sa'anni na kasashen Qatar da China suke tafiya domin taka leda saboda shekarunsu sun ja, amma ni gani a wannan babban kulob.

Zan ci gaba da yin iya kokari na domin ganin mun ci gaba da lashe kofuna a kowanne mataki".

A makon jiya ne dan wasan ya koma kungiyar Juventus ne a kan fan 99.2 bayan ya yi shekara tara a Real Madrid.

Cristiano Ronaldo ya ce wata kila shi ne zai lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya wato Ballon d'Or.

"Na koma wannan kungiyar a wannan lokaci. Ina matukar farin ciki," a cewarsa.

Har ila yau ya ce yana fatan kasancewa "mai sa'a" yayin da kungiyar take fafutikar lashe Gasar Zakarun Turai.

Albashin Ronaldo a Juventus

Naira biliyan 50 aka sayo shi

N12.5b

A shekara

Naira 1b

A duk wata

 • N258m A duk mako

 • N36m A duk rana

 • N1.5m A duk awa daya

 • N12m A awanni takwas na baccinsa

Getty

Ronaldo, wanda sau biyar yana lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya, ya ci wa Madrid kwallaye 450 ne - kuma sau hudu yana lashe Kofin Zakarun Turai da kuma La Liga biyu.

"Ina so na yi nasara, ina so na zama fitacce. Wa ya sani watakila kila na kara lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya, amma haka rayuwa za ta ci gaba da tafiya da kanta," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Samun hakan yana da wuya a Manchester da Real Madrid, amma watakila na sake samu a nan, za mu gani."

Dan wasan kasar Portugal din ya ce akwai abubuwa da dama da suka sanya shi ya amince ya koma Juventus.

Bajintar Ronaldo

Bayanan hoto,

Sau biyar Cristiano Ronaldo yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or

 • Ronaldo ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Madrid
 • Ya ci kwallaye 105 a gasar Zakarun Turai
 • Kwallaye 311 a gasar La Liga
 • Kofi 16 a Real Madrid da suka hada da La liga biyu da Zakarun Turai hudu da gasar duniya ta kungiyoyi
 • Ya ci kwallaye uku-uku (hat-tricks) shi kadai sau 44, kuma sau 34 a La Liga
 • Sau takwas yana cin kwallaye fiye da hudu a Real Madrid
 • Ya taba cin kwallaye 61 a kakar 2015-16 a dukkanin wasanin da ya buga
 • Hakan ya hada da kwallaye 48 a La Liga
 • Kwallaye 659 ya ci a rayuwarsa - biyar a Sporting Lisbon, da 118 a Manchester United da 451 a Real Madrid da 85 a Portugal
 • Sau biyar yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or