Arsenal za ta rage 'yan wasa, United za ta rasa Gareth Bale, Ahmed Musa ya yi kasuwa

Eden Hazard
Bayanan hoto,

Eden Hazard ya taka rawar gani a gasar kofin duniya

Kocin Belgium, Roberto Martinez, ya gaya wa dan wasan Chelsea, Eden Hazard, mai shekara 27, cewa ya zama dole ya yi tunanin barin Stamford Bridge, yayin da Real Madrid ke zawarcinsa, in ji Mirror.

Amma sabon kocin Chelsea, Maurizio Sarri, yana sa ran rike dan wasan gaban Belgium, Eden Hazard da mai tsaron gidan Belgium, Thibaut Courtois da dan wasan tsakiyar Brazil, Willian da kuma na Faransa N'Golo Kante bayan irin bajintar da suka nuna a gasar kofin duniya, in ji Sun.

Manchester United tana gab da kasa sayen Gareth Bale, yayin da ake tsammanin cewar sabon kocin Real Madrid Julen Lopetegui zai shaida wa mai shekara 29 din cewar yana da muhimmanci a jerin 'yan wasan da yake so ya yi amfani da su a kulob din, kamar yadda Metro ta rawaito.

Bayanan hoto,

A da dai rahotanni na cewa Gareth Bale na son barin Real Madrid

Sabon kocin Arsenal, Unai Emery, yana shirin rage 'yan wasan kulob dinsa - kuma makomar dan wasan gaban Ingila Danny Welbeck, mai shekara 27, da kuma mai tsaron gidan Colombia, David Ospina, mai shekara 29, na cike da shakku, a cewar Telegraph.

Ana alakanta dan wasan gaban Leicester kuma dan Najeriya, Ahmed Musa, mai shekara 25, da komawa kungiyar kwallon kafar Al Nassr ta Saudiyya kan kudi fam miliyan 40, in ji Leicester Mercury.

Bayanan hoto,

Ahmed Musa ya zama dan kwallon da ya fi ci wa Najeriya kwallo a gasar kofin duniya

Manchester City ta ki biyan fan miliyan 80 da Real Madrid ke nema kan dan kasar Croatia da ke wasan tsakiya, Mateo Kovacic, in ji Sky Sports.

City na bukatar sayen dan wasan tsakiya domin kara karfin tawagarta musamman bayan da Yaya Toure ya bar kungiyar.