Courtois zai tafi Madrid, Zidane zai koma Juve, Man U na son Arnautovic

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hazard ya ce ba shi da "matsala" a Chelsea, duk da cewa ana alakanta shi da komawa Real Madrid

Real Madrid ta sanya dan wasan gaba na Chelsea da Belgium Eden Hazard, mai shekara 27, a sahun gaba na jerin 'yan wasan da suke so su maye gurbin Cristiano Ronaldo, wanda ya koma Juventus, a cewar jaridar (Star).

Ana sa ran dan wasanChelsea da Belgium Thibaut Courtois, mai shekara 26, ya koma Real Madrid a kan fan miliyan 31, a cewar jaridar Marca.

Idan suka sayar da Courtois, Chelsea za su duba yiwuwar sake sayen tsohon golansu mai shekara 36 dan kasar Czech Petr Cech daga Arsenal, ko kuma golan Leicester dan Denmark Kasper Schmeichel, mai shekara 31, in ji (Sky Sports).

Wolves da Fulham na son sayen dan wasan Manchester City Oleksandr Zinchenko, mai shekara 21, duk da cewa dan kwallon na Ukraine ya bi City zuwa atisayen da suke yi a Amurka, in ji (Mirror).

Dan wasan baya na Ingila Gary Cahill, 32, zai iya barin Chelsea saboda kulob din na neman dan bayan Juventus mai shekara 23, Daniele Rugani kan fan miliyan 44, a cewar jaridar (London Evening Standard).

Kuma har yanzu Chelsea na son sayen golan Roma Alisson duk da cewa Liverpool ta tayashi fan miliyan 62, in ji (Football Italia).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marko Arnautovic ya taka rawa sosai a West Ham a kakar da ta gabata

Dan wasan West Ham Marko Arnautovic ka iya komawa Manchester United ko Roma, saboda kulob din a shirye ya ke ya saurari bukatar masu son sayen dan kwallon na kasar Austria, a cewar TalkSport.

Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 46, zai koma Juventus, kulob din da ya murza wa leda daga shekarar 1996 zuwa 2001, a matsayin mai bayar da shawara, in ji jaridar Libertad Digital.

An shaida wa kocin Newcastle United Rafael Benitez cewa sai ya sayar da wasu 'yan wasan tukunna kafin a bashi damar sayan wasu, in ji Daily Mirror.

Crystal Palace na dab da kammala cinikin dan wasan Senegal Khouma Babacar, mai shekara 25, daga Sassuolona Italiya kan fan miliyan 12, kamar yadda Daily Mirror ta rawaito.

Karin labaran wasanni

Labarai masu alaka