Donald Trump: Ba na tsoron Vladmir Putin

Donald Trump Hakkin mallakar hoto EPA

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa Rasha ta yi kokarin yin katsalandan a zaben Amurka na 2016, zaben da ya ba shi damar zama shugaban kasa.

Amma a yayin wani taron koli da ya yi da takwaransa na Rasha Vladmir Putin ranar Litinin, Mista Trump ya fadi akasin haka ne.

Wannan katobarar ta janyo damuwa daga 'yan majalisar kasar, har daga masu goyon bayansa.

Shugaba Trump na karkashin tsaninin matsi domin ya bayyana kalaman da yayi da suka daure kawunan shugabannin duniya, kuma suka fusata 'yan jam'iyyrsa ta Republican.

A yayin da yake ganawa da shugaban Rasha Vladmir Putin ranar Litinin, ya kasa takalarsa game da batun kutsen da ake tuhumar Rashr da yi ma tsarin zaben Amurka na 2016.

A madadin haka, sai ya goyi bayan sukar da Mista Putin din yayi cewa tuhumar da hukumomin tsaron kasar ke yi ma Rashar abin dubawa ne.

Mista Trump yayi kokarin kare kansa daga zargin cewa yana tsoron Mista Putin ne, inda ya ce tuntube harshe ne ya sa ba a fahimce shi ba.

Ya kuma ce gwamnatinsa na daukar abin da ya kira 'kwakkwaran mataki' domin kare muradun Amurka da tsarin zabukanta daga duk wata barazana, amma da alama 'yan jam'iyyarsa ba su gamsu ba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Mitch McConnell ya fito fili ya gargadi Rasha da kada ta kuskura ta sake gwada kutsen da ta yi a 2016.

Kana shugaban majalisar wakilai Paul Ryan ma ya nemi Mista Trump da ya rage soyayyar da yake nuna wa abokiyar gabar Amurkar wato Rasha.

Labarai masu alaka